29 Afirilu 2026 - 20:56
Source: ABNA24
Taya Murna Da Haihuwar Imam Aliyur Ridha As

11 Ga Zulqahdah 148h A Irin wannan rana ne wanda ta kama juma’ah ko Alhamisa ga wannnan wata aka a birni madina aka haifi Imam Aliyurridah As

Imam As kamar yadda yake sanannan abune shine Imami na 8 cikin jerin Imaman Shiriya da Annabi sawa ya barwa Al’ummar anai masa Alkunya da Arridha, Sabir, Rady da  abunda yasa ake ce masa Arridah yakasance yaradaddaen Allah ne asamansa kuma yardadden Annabin Muhammada sawa da iyalan sa a doron kasa a wata fadar kum ance saboda yardaddae ne ga wanda ya saba masa dama wanda ya yarda dashi 

Mahaifin shine Imam Musal Kazim As Mahifiyar sa kuma ana kiranta da Najmah’ Takattum Imam yayi zamani da Khalifofin Abbasawa guda uku Harunarrsahid da Muhammadul Ameen da Abdullahi Ma’amuun. Kamar yadda yake Imam yataso da tabiyya ta gidan Annabta kamar yadda sauran Aimmah As bayan samun cikkakkaiyar tarbiya Imam yakansance ma’abocin Kwarjini da daukaka acikin Al’ummar da yake zaune da ita musamman mutane Madina inda mutane suke girmama shi matsayinsa na dan manzon Allah sukan kirashi da Yabna Rasulallah sukan sauarri bayanonin tare da zama tare dashi. Imam ya Rayu tsawon shekaru 55 inda dauki shekara 20 yana Imamanci Al’ummar Annabin sawa.

Imam as yayai munazarori da dama alaokcin rayursa da wasu daga cikin malamai na wannan lokacin  musamman bayan zuwan Maru Kurasan fadar mulkin Ma’amun inda Ma’amun din ya shiraya masa wasu Munazarori da malaman Addinai na lokacin sa inda mutane da sauran malamai suka halarci wadannan jerin munazarorin wanda Imam As adukkan su ya kayar da abokan munazarar sa har saida suka yarada fifikon sa akansu wanda malamai sunce dalilin wannan munzarori shine domin Khalifa ya kore tunanin cewa Aimmah suna da Ilimin kai tsaye daga wajen Ubangiji inda Imam ya Tabbatar masu dahakan ta hanyar basu amsa na dukkan abunda suka tambayeshi inda su kuma suka kasa bashi amsa ga abunda ya tambayesu.

Sakamakon rikicin dake faruwa tsakanin A’immah da mabiyansu da kuma Banil Abbas tare da fifikon da matsayi da sukaga Imam as yana dashi ciokin Al’ummah wanda ya mafi na Khalifa kansa hakan yasanya khalifa tunnanin kawar dashi inda yasamu nasara hakan ta hanyar sanya masa guba ahnayarsu ta dawo daga Maru Kursan zuwa Bagdad Inda yayi Shahada aka binne shi wurin da yanzu ake cema masa mashahad dake kasar Iran.

Your Comment

You are replying to: .
captcha